1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Prodi ya tsallake kuri´ar farko da sabuwar gwamnatinsa ta fuskanta

Sabon FM Italiya Romano Prodi ya tsallake wani gwaji na farko a matsayin sa na sabon FM wannan kasa, inda ya lashe kuri´ar amincewa da gwamnatinsa da majalisar dattijai ta kada. ´Yan majalisa 165 suka kada kuri´ar amincewa yayin da 155 suka nuna adawa da gwamnatin ta masu matsakaicin ra´ayin sauyi. Da farko Mista Prodi ya yi kira ga ´yan majalisar dattijan da su marawa gwamnatinsa baya, kwana daya bayan ya bayyana shirye shiryen sa wadanda suka hada da janye dakarun Italiya daga Iraqi tare da bullo da sahihan matakan farfado da tattalin arzikin kasar. Prodi ya ce gwamnatin sa kwakkwara ce duk da cewa rinjayen kujeru biyu kadai ta samu a zaben da aka gudanar cikin watan da ya gabata.