1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Praministan Habasha ya ki amicewa da belin jagororin jam´iyun adawa

November 9, 2005
https://p.dw.com/p/BvLr

Praministan kasar Habasha Meles Zenawi, yayi watsi da kiran da kasashenTurai da Amurika su ka yi masa, na belin dubbunan mutanen da jami´an tsaro su ka capke, a makon da ya gabata, a sakamakon zanga zangar da jam´iyun adawa su ka shirya a wannan kasa.

Praministan ya ce, shuwagabanin jam´iyun adawa, da a halin yanzu, a ke tsare da su, a na tuhumar su ne, da cin amanar kasa, wannan kuma, baban lefi ne, da ke iya kai har ga hukunci kissa.

Meles Zenawi ,ya tabatar da cewa, kotu zata gurfanar da su, ta kuma yanke masu hukuncin da ya dace.

A cikin zanga- zangar, jami´an tsaro, sun yi awon gaba, da kusoshin jam´iyar adawa ta CUDP su 24.

Yan adawa sun shirya wannan zanga zanga, domin kin amincewa da sakamakon zaben yan majalisun dokoki na watan Mayu da ya wuce, wanda acewar su, ke cike da magudi.

Mutane fiye da 50 su ka rasa rayuka a cikin arangamar da a kayi, da jami´an tsaro, a makon da ya wuce.