1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka tsakanin Poland da hukumar EU

Yusuf BalaJanuary 10, 2016

Dubban jama'a a ranar Asabar sun yi zanga-zanga a kasar ta Poland don yin adawa da sabbin matakan yin tsangwama ga kafafen yada labarai.

https://p.dw.com/p/1HayV
Rolf Wilhelm Nikel - deutscher Botschafter in Polen
Rolf Wilhelm Nikel jakadan Jamus a PolandHoto: picture-alliance/dpa/A. Burgi

An bukaci jakadan kasar Jamus Rolf Wilhelm Nikel da ke a birnin Warsaw ya je dan ganawa da ministan harkokin kasashen waje na Poland Witold Waszczykowski, wannan na zuwa ne bayan da 'yan siyasa a kasar ta Jamus suka yi suka ga tsare-tsaren da Poland ke zuwa da su musamman na neman hana fadin albarkacin baki.

Tun da fari ministan shari'a a kasar Poland ya yi watsi da sukar da hukumar tarayyar Turai ta yi wa sabon tsarinsu da ya shafi tsare-tsaren kafafan yada labarai inda ya bayyana tuhumar da ake wa kasar ta Poland da cewa babu tunani a cikinta, wani lamari da ya kara nuna tsamin dangantaka tsakanin kasar da mahukuntan na EU da ma kasar da shugabanta ya fito.

Minista Zbigniew Ziobro ya sanya ayar tambaya kan tarihin mahukuntan Berlin inda a kaikaice ya tabo lokacin mulkin 'yan Nazi da ma mamayar da Jamus ta yi wa Poland a lokacin yakin duniya na biyu cikin sakon da ya aika wa Gunther Oettinger da ke zama kwamishina a hukumar ta EU daga Jamus.

Dubban jama'a a ranar Asabar sun yi zanga-zanga a kasar ta Poland don yin adawa da sabbin matakan yin tsangwama ga kafafen yada labarai da kutunan kasar suka dauka na hanasu gudanar da aiki yadda ya dace.