1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Philippines: Duarte ne sabon shugaban kasa

Umaru Aliyu/ASMay 10, 2016

Bayan kidaya galibin kuri'un da aka kada a a zaben shugaban kasa na Philipines hukumar zaben kasar ta bayyana Rodrigo Duarte a matsayin wanda ya samu nasara.

https://p.dw.com/p/1IlCH
Philippinen Präsidentschaftskandidat Rodrigo Duterte
Hoto: Reuters/E. de Castro

A lokacin da aka gabatar da sakamakon, hukumar zaben kasar ta ce na wucin gadi ne amma kuma canjin da za a samu daga abin da ke hannu yanzu ba zai zama mai yawa ba don haka Duarte da ke da kuri'u mafiya rinjaye shi ne sabon shugaban kasar. Tun da aka sanar da yadda zaben ya kasace, wadanda suka yi hamayya da Duarte din suka amince da shan kaye kana suka tayashi murna.

Ji kadan bayan fitar sakamakon na wucin gadi, Duarte wanda tsohon magajin gari ne na birni Davao ya bayyana gaban dimbin magoya bayansa a babban birnin kasar Manila inda ya nuna godiya garesu saboda zabensa da suka yi. Ya kuma godewa sauran yan takara wadanda suka mika wuya kana suka amsa kayen da suka sha a zaben.

Daya daga cikin al'amuran da sabon shugaban kasar ta Philippines ya ce sun masa dadi a wannan lokaci shi ne yadda abokan hamayyarsa suka nuna halin dattaku bayan fitar sakamakon zaben har ma ya ke cewa ''hakan kyakkyawar al'ada ce da babu shakka za ta hana aukuwar duk wani tashin hankai na siyasa.''

Philippine Rodrigo Duterte
Sabon shugaban Philippines Rodrigo Duarte ya lashi takobin kawar da manyan laifukaHoto: picture alliance/dpa/F.-R. Malasig

Duarte mutum ne mai matsanancin ra'ayi wanda kuma a lokacin yakin neman zabe ya yi alkawarin gabatar da dokar hukuncin kisa ga duk wadanda aka samu su na aikata manyan laifuka kuma ya ce zai kawo karshen aikata irin wadannan laifuka a kasar ta Philippines tsakanin watanni shida da kama mulkinsa. A tsawon shekaru 2 da ya yi kan mukamin magajin garin Davao, Duarte ya yi suna a matsayin mai yaki da aikata manayan laifuka ko da ya ke an sha zarginsa da laifukan bada izinin kisan jama'a ba tare da shari'a ba.