1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paul Wolfowitz ya kiri turai da Amurika su buda kofofin kasuwannin su

Shugaban bankin Dunia Paul Wolfowitz, yayi kira ga kasashe masu hannu da shuni, da su buda kofofin kasuwanin ga kasashe matalauta na Afrika da na sauran dunia.

A wannan jawabi da yayi ,a shiryen shiryen fara taron kungiyar cinikaya ta Dunia, WTO ko kuma OMC sati mai zuwa, ya kara da cewa, balle shingyen cinikaya, itace hanya daya, mai kwari da za ta tallafawa kasashen, sun kubuta daga hayin talaucin da su ke fama da shi.

Ya bada misali da kasar Bangladesh, daya daga kasashe mafi talauci a dunia, wadda a shekara, ta ke shigar da kaya Amurika na kimanin dalla billiard 2, da kuma Faransa dake shigar da kaya na dalla billiard 30, a shekara zuwa kasar ta Amurika, kasashen 2, ba biyan kudaden custum kokuma Duwan, daidai duk da banbanci da ke akwai, na yawan kayan da su ke shigar da su.

A hannu daya, Paul Wolvowitz yai kira ga kasashen turai, da Amurika, da su takaita tallafin kudaden da su ke baiwa manoman su ,wanda ko shaka babu, ke kara talauta Afrika.