Paragai: Dokar zabe ta jawo kone majalisa | Labarai | DW | 01.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paragai: Dokar zabe ta jawo kone majalisa

Shugaba Horacio Cartes na neman a samar da sauyi a kundin tsarin mulkin kasar domin samun dama ta sake zabensa idan wa'adin mulkinsa ya kare a karshen shekarar 2018.

A ranar Juma'a 'yan majalisar dattawan kasar Paragai sun amince da doka da za ta ba wa shugaban kasar dama ta a sake zabensa, lamarin da ya sanya masu zanga-zanga suka afka zauran majalisa da tarwatsa ambobinta bayan karya kofar shiga da fasa tagogi har ma da sanya wuta a wasu sassa na ginin.

Shugaba Horacio Cartes na neman a samar da sauyi a kundin tsarin mulkin kasar domin samun dama ta sake zabensa idan wa'adin mulkinsa ya kare a karshen shekarar 2018.

Masu goyon bayan shugaban dai sun amince da kudirin dokar a ranar Juma'a duk kuwa da fiskantar tirjiya daga bangaren adawa wadanda ke cewa bude kofa ce kawai ta mulkin kama karya a kasar. Hakan dai ya sanya daruruwan masu zanga-zanga fantsama tituna da ma afkawa ginin majalisar.

Tun dai a shekarar 1992 kasar ta yi watsi da batun sake zaben shugaban kasa a kokari na kaucewa dawowar mulkin danniya a kasar.