1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma yayi kira ga Majalisar Dinkin Duniya

January 1, 2006
https://p.dw.com/p/BvEB

Pope/New Year

Shugaban kiristoci mabiya darikar katholika na duniya

Paparoma Benedict na goma sha shida yayi kira ga majalisar dinkin duniya data zage damtse wajen tabbatar da adalci da hadin kai da kuma zaman lafiya a duniya.

A sakon sa na farko na sabuwar shekara wanda ya gabatar a fadarsa ta Vatican Paparoman yace sakamakon rashin adalci da tashe tashen hankula a sassa daban daban na duniya wajibi ne a hada kai domin tabbatar da zaman lafiya.