1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma yayi kira a samar da zaman lafiya a duniya

July 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuFp
Paparoma Benedict na 16 a yau lahadi yayi kira da a samar da zaman lafiya yana mai cewa ya kamata kasashe su daina rikice-rikice a duniya don kirkiro abin da ya kira wata aljanna a doron kasa. A jawabin da yayi a gaban masu ibada da suka hallara a wurin shakatawarsa dake Italiya Paparoma ya ce hutun da yake yi a wannan lokaci na zafi ya kara janyo hankalinsa ga wahalhalu da matsalolin da yake yake ke haddasawa.