1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma ya koka kan halin da Rohingyas ke ciki a Bama

Gazali Abdou Tasawa
August 27, 2017

Jagoran Kiristoci mabiya darikar Katolika Paparoma Farancis ya bayyana goyon bayansa ga tsirarun Musulmi 'yan kabilas Rohingyas na kasar Bama dangane da wariya, kyama da kuma cin zarafin da suke fuskanta a kasar.

https://p.dw.com/p/2ivXU
Vatikan Papst Franziskus  Tag gegen Menschenhandel
Hoto: Getty Images/AFP/T. Fabi

Jagoran Kiristoci mabiya darikar Katalika Paparoma Farancis ko Francois ya bayyana goyon bayansa ga tsirarun Musulmi 'yan Kabilas Rohingyas na kasar Bama  dangane da wariya, kyama da kuma cin zarafin da suke fuskanta daga sauran al'ummar kasar ta Bama. Paparoma Francis ya bayyana wannan matsayi nasa ne a gaban dubunnan Kristoci a lokacin wani taron addu'o'i a wannan Lahadi