1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma ya kammala ran gadi a Turkiyya

Pinado Abdu WabaNovember 30, 2014

Yawan 'yan gudun hijira da rigingimun kasashe da dama sun dauki hankalin Paparoman lokacin wannan ziyarar ta sa musamman ma harin da aka kai a masallacin Kano.

https://p.dw.com/p/1DxMn
Papst Franziskus in Istanbul 30.11.2014
Hoto: Reuters/U.Bektas

Paparoma Francis ya kebe lokaci cikin ziyarar da ya kai Turkiyya dan ganawa da masu gudun hijira daga Iraki da Siriya da shugabanin addinai daban-daban. Paparoman wanda ganin yawan 'yan gudun hijiran ya sosa mi shi rai, ya bayyana takaicinsa ga irin yadda radadin rikice-rikicen da ke faruwa ke tasiri sosai a kan talakawa. Bayan sujadar da suka yi da safiyar yau a babban cocin mabiya darikar orthodox, karkashin jagorancin babban limaminsu Bartholomew na daya na Constaninople Paparoma Francis ya yi adduo'i kuma ya yi jawabi kamar haka:

"Kasashe da dama na fama da yaki. Ina matukar tausayin mutanen da wannan yanayi ya ritsa da su, musamman ma na baya-bayan nan harin da aka kai kan wadanda ke sallar juma'a a babban masallacin jihar Kano a Najeriya"

Paparoman ya kuma gana da shugaban Yahudawan yankin wadanda adadinsu ke cigaba da raguwa. Daga karshen wannan ziyara dai, Barthalomew na daya na Constantinople da Paparoma Francis sun rubuta takardar kawo karshen ziyarar, inda suka yi kira ga kowani darika da addini da ya mutunta hakkokin dan adam domin tabbatar da rayuwa cikin adalci da kwanciyar hankali.