1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma ya jagoranci addu´o´in jajiberen Kirismeti a St. Peters

December 25, 2005
https://p.dw.com/p/BvF7

Paparoma Benedict na 16 ya jagoranci addu´o´in jajiberen ranar bukin Kirismeti na farko a matsayin sa na shugaban mabiya darikar Katholika na duniya. Kimanin maziyarta dubu 10 ne suka hallara a cikin majami´ar St. Peters dake birnin Rom yayin da wadanda ba su samu shiga cikin majami´ar ba kuma suka kalli bukin addu´o´i a wani katafaren allon telebijin da aka kafa a wajen harabar majami´ar ta St. Peters. Paparoman yayi kira ga mabiya darikar katholika a duniya da su zama manzannan zaman lafiya musamman a wannan lokaci da tashe tashen hankula suka zama ruwan dare a duniya baki daya. Bugu da kari Paparoman yayi wata addu´a ta musamman don kawo karshen rikicin yankin GTT. Daruruwan miliyoyin mutane a kasashe sama da 50 suka kalli bukin addu´o´in na holimass kai tsaye ta akwatunan telebijin su.