Paparoma ya isa a sansanin Moria da ke a Girka | Labarai | DW | 16.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma ya isa a sansanin Moria da ke a Girka

Paparoma Francis tare da rakiyyar shugabannin Cocin Orthodox na Girka sun gana da 'yan gudun hijirar a sansanin Moria

Paparoma wanda ya tattauna da 'yan gudun hijirar ya ce zai koma fadar Vatican cikin jirgin sama tare da wasu daga cikin 'yan gudun hijirar iyale har guda goma. Waɗanda suka zo kafin 20 ga watan Maris kafin a cimma yarjeniyar EU da Girka wadanda kuma aka yi wala-wala wajen tattance waɗanda za su samu alfarmar.

An shirya Paparoman zai jagorancin wasu aduo'i a bakin teku domin tunawa da 'yan cirani da suka mutu a lokacin da suke ƙoƙarin tsallakawa zuwa Turai cikin jiragen ruwa marasa inganci kimani su 375 yara ƙanana a shekara bara.