Paparoma ya fara ziyara a Kenya | Labarai | DW | 25.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma ya fara ziyara a Kenya

Birnin Nairobin kasar Kenya dai ita ce a kafar farko da shugaban darikar roman katolikan ya fara yada zango, a rangadin da zai yi a kasashe uku na Afirka.

Da yammacin yau ne ake saran Paparoma Francais zai gana da shugaba Uhuru Kenyata na Kenya, kafin ya jagoranci sajadar da mutane sama da dubu 500 za su halarta a gobe Alhamis.

Bayan kwanaki biyu a Kenya, shugaban darikar katolika mai shekaru 78 da haihuwa, zai shige zuwa kasar Yuganda kafin Janhuriyar Afirka ta tsakiya. Ziyarar da ake saran zai kammala ranar Litinin.

A kwai kimanin mabiya darikara roman katolika miliyan 180 a fadin nahiyar Afirka. Ziyarar ta paparoma Francis dai, ita ce ta 11 irinsa a wajen fadarsa ta Vatikan dake birnin Rome, tun da ya hau wannan mukami a shekara ta 2013.