Paparoma Francis ya buƙaci Kiristoci da su yi juriya | Labarai | DW | 27.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paparoma Francis ya buƙaci Kiristoci da su yi juriya

Jagoran ɗarikar Roman Katolika Paparoma Francis ya yi kira ga mabiya addinin Kirista da su kasance masu juriya da kuma tsammanin samun sa'ida.

Jagoran ɗarikar Roman Katolika Paparoma Francis ya yi kira mabiya addinin Kirista da su kasance masu juriya da kuma tsammanin samun sa'ida.

Paroma ya bayyana haka ne a daran jiya a lokacin da ya jagorancin wasu adu'o'i na bubukuwan Easter na farkon mako a majami'ar Saint Pierre. Paparoman wadan ya sha nanata waɗannan kallamu na juriya har kusan so 20 a lokacin adu'o'in. Yana yin tsokaci game da irin hare-haren da aka yi fama da su a baya-baya a Beljiyam.