1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

May 28, 2014

Zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban daban musamman rikicin Izra'ila da Palesdinu ne ya mamaye ziyarar da Paproma Francis ya kai yankin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/1C8Dg
Hoto: Reuters

Shi dai shugaban darikar Roman Katolika ta duniya Paparoma Francis ya yi addu'a a muhimmin gurin ibada na yahudawa da ke birnin kudus, kafin ya tattauna da abokansa na Birnin Buenos Aires, wadanda ba wasu ba ne illa limamin yahudawa Abraham Skorka da kuma Omar Abboud wanda musulmi ne. Da ma dai hanyoyin samar da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban daban a yankin gabas ta tsakiya ne babban abin da ajendar tasa ta kunsa.

Sai dai kuma batutuwan da suka jibanci siyasa sun ta kunno kai a wannan ziyarar da Paparoma ya gudanar a Izra'ila. Shi dai paparoman ya yi kira da aka kawo karshen rikicin da ke yawan aukuwa tsakanin musulmi da kuma kiristocin a yankin gabas ta Tsakiya. Ma'ana tsakanin Isra'ilada kuma Palesdinawa. Sannan kuma ya bukaci a sakar wa musulmi da kirostoci da kuma yahudawa marar gudanar da ibadarsu a wurare masu tsarki na birnin Kudus ba tare da tsangwama ba.

Wannan dai ba ya rasa nasaba da kiran da babban mufti na birnin Kudus Mohammed Hussein ya yi wa paparoman, inda ya nemi da ya goyi bayan gaggawarmayar da Palesdinawa ke yi na nemar wa kansu kasa mai cin gashin kanta. Ya ce " Ta wannan hanya ce kiristoci da musulmi da yahudawa za su samu damar ziyartar wurare masu tsarki na addinansu."

Batun rikicin Izra'ila da Palesdinu

Da ma dai tun da farko Paparoma Francis ya nunar da cewa ba wani yunkurin kirki ake yi don samar da zaman lafiya tsakanin Isra'aila da kuma Palesdinawa. Saboda haka ne ya gana da manyan limaman musulmi da na yahudawa na birnin Kudus, da kuma babban limanin 'yan Orthodox, a wani mataki da shi paparoma Francis ya danganta a mutunta mabiya addinai daban daban na duniya.

"Ba wai kyautata dangantaka tsakanin kiristoci da kuma yahudawa kawai ake bukata ba, amma kuma akwai bukatar mu yi karatun ta nitsu, mun tambayi kanmu ma'anar imanin da ke tattare da mu."

Shugaban darikar Roman katolikta ta duniya ya ziyarci gidan adana kayan tarihin yahudawa da 'yan Nazi suka yi wa kisan kare dangi a zamanin yakin duniya na duniya. Paparoma Francis ya roki Allah da ka da irirn wadannan kashe-kase su sake aukuwa a duniya.

Shi dai Paparoma Francis, shi ne shugaban darikar Roman katolika na hudu a duniya da ya taba kai ziyara kasar izra'ila a cikin tarihi.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Umaru Aliyu