1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Papa Roma na kai ziyara a ƙasar Poland.

May 25, 2006
https://p.dw.com/p/Buwm

A ci gaba da ziyarar kwana 4 da yake kai wa ƙasar Poland, Papa Roma Benedict na 16, ya yi kira ga mabiya ɗariƙar Katolika na ƙasar, da su fid da tunanin muzgunawar da aka yi wa jama’an ƙasar a lokacin mulkin kwaminisanci, daga zukatansu. Wannan zamanin, inda aka yunƙuri rarraba kawunan ’yan ƙasar, ya wuce, inji Papa Roman. A cikin huɗubar da ya yi wa wani taron ibadan da aka shirya, a majami’ar St. John da ke birnin Warsaw, Papa Roman ya bukaci mabiya ɗariƙar da su yafe wa tsoffin jami’an leƙen asirin ƙasar, duk irin laifuffukan da suka yi musu. Ana dai hasashen cewa, kusan limaman cocin katolikan dubu 8 da ɗari 5 ne suka ba da haɗin kai ga Hukumar Mulkin Kwaminisanci ta ƙasar a da.

Shugaban ɗariƙar Katolikan, ya kuma bayyana farin cikinsa da sake dawowa ƙasar, da cewa:-

„Na dai yi ta begen kawo ziyara a wannan ƙasar da kuma kasancewa cikin wannan al’umman, inda daga cikinsu ne wanda na gada a aikin bauta wa Ubangiji, marigayi John Paul na biyu yake. Na zo ne, don in bi diddigin halin rayuwarsa, tun yana ɗan yaro, har zuwa lokacin da ya tashi zuwa taron Vatican da aka yi a 1978, inda aka naɗa shi Papa Roma.“

Wannan dai ita ce ziyara ta biyu da Papa Roman, Benedict na 16, ya kai a ƙasar ta Poland, tun da aka naɗa shi a wannan muƙamin, a watanni 13 da suka wuce. Gobe juma’a ne kuma, zai jagoranci wani babban taron ibada da za a yi a fili a birnin na Warsaw, kafin ranar lahadi kuma, ya ziyarci tsohon sansanin gwale-gwalen nan da ’yan Nazi suka kafa a garin Auschwitz.