Papa Roma, Benedict na 16, ya shugabanci wani taron addu’a na ƙasa da ƙasa don samad da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya. | Labarai | DW | 23.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Papa Roma, Benedict na 16, ya shugabanci wani taron addu’a na ƙasa da ƙasa don samad da zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.

Shugaban ɗariƙar Katolika, Papa Roma Benedict na 16, ya yi kira ga tsagaita buɗe wuta kai tsaye a Gabas Ta Tsakiya tare kuma da kai taimakon agaji cikin gaggawa ga ƙasar Lebanon, wadda bisa cewarsa, yaƙi ta ragargaza.

Da yake yi wa ɗimbin yawan jama’an da suka halarci wani taron ibada na ƙasa da ƙasa a garin Les Combes huɗuba, Papa Roman, ya ce yana taya ɗimbin yawan fararen hular da wannan bala’in ya shafa juyayi, fararen hular da ya ce ba su san shiga ko fita cikin wannan lamarin ba. Ya kuma nanata cewa ’yan ƙasar Lebanon ɗin na da ’yancin zama cikin lumana a ƙasarsu, kamar dai yadda al’umman Isra’ilan ke da shi. Kazalika kuma, ya ce al’umman Falasɗinawa ma na da ’yancin samun ƙasarsu mai cin gashin kanta. Gabannin taron ministocin harkokin wajen ƙasashen yamma da za a yi a birnin Rome a ran laraba mai zuwa, shugaban ɗariƙar Katolikan, ya yi kira ga gamayyar ƙasa da ƙasa da ta samo hanyoyin fara shawarwari tsakanin ɓangarorin da ke yaƙan junan a Gabas Ta Tsakiya.