Paolo Gentiloni ya zama sabon Firaministan Italiya | Labarai | DW | 11.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Paolo Gentiloni ya zama sabon Firaministan Italiya

Shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella, ya nada ministan harkokin wajen kasar Paolo Gentiloni a matsayin Firaministan kasar wanda ya canji Matteo Renzi da ya yi murabus

Shi dai sabon Firaministan na Italiya Gentiloni mai shekaru 62 a duniya, ana yi masa kallon na kusa da tsohon Firaminista Matteo Renzi mai murabus, wanda kuma jam'iyyarsa ta (DP) "Demokaratique Parti " ta saka shi a sahun gaba daga cikin wadanda take son su karbi wannan mukami. A jawabinsa na farko bayan bashi wannan mukami, sabon Firaministan na Italiya cewa ya yi:

"Ina mai imanin da bukatun da ke garemu cikin gaggawa na bai wa kasar Italiya sabuwar gwamnati mai cikeken iko, wadda za ta bai wa al'ummar kasar kwarin gwiwa da kuma fuskantar manyan kalubale da suka hada da hulda ta kasa da kasa, tattalin arziki da kuma al'umma kuma  dukkannin su cikin daukar niya da aiki tukuru."