Panama ta samu kujera a Kwamitin Sulhun MDD | Labarai | DW | 07.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Panama ta samu kujera a Kwamitin Sulhun MDD

Kasar Panama ta samu kujerar wucin gadi a kwamitin sulhun MDD. Babbar mashawartar majalisar ta dinkin duniya ta zabi kasar ta Panama a zagaye na 48 na kuri´un da aka kada, wanda hakan ya kawo karshen kiki-kaka ta aka shafe makonni da dama ana yi akan kasar da zata dare kan kujerar yankin Latun Amirka da Caribian a kwamitin sulhun. A kuri´un har 47 da aka kada da farko babu daya daga cikin kasashen Guatemala wadda Amirka ke goyawa baya da Venezuela karkashin jagorancin shugaba Hugo Pervez mai sukar limirin Washington, da ta samu rinjayen kashi 2 cikin 3 da take bukata don darewa kan wannan kujera.