Pakistan ta fusata game da farmakin da Amirka ta kai akan wani kauyen kasar
January 14, 2006Pakistan ta mika takardar nuna fushinta a hukumance ga ofishin jakadancin Amirka dangane da mutuwar ´yan kasar su akalla 18 a wani farmakin da jiragen saman yakin Amirka suka kai da nufin halaka mataimakin shugabab kungyiar al-Qaida Ayman al-Zawahiri. Jami´an Pakistan dake gudanar da binciken don gano ko an halaka na hannun damar Osama Bin Laden a wannan farmaki, sun ce bai mai yiwuwa ba ne al-Zawahiri na cikin kauyen na Pakistan a lokacin da aka kai harin. Kafofin yada labarun Amirka sun rawaito wasu jami´an leken asiri na cewa an auna wannan hari ne akan al-Zawahiri. To amma mazauna yankin sun ce dukkan wadanda aka kashe a harin ´yan kabilar yankin ne kuma daukacinsu mata ne da kananan yara. A yau mutane kimanin dubu 5 sun gudanar da taron gangami a filin wasan yankin Bajur don yin Allah wadai da harin.