1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta ƙaddamar da bincike kan harin ƙunar baƙin wake a Islamabad

July 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuFG

An tsaurara matakan tsaro a Islamabad babban birnin kasar Pakistan yayin da gwamnati ke gudanar da bincike bayan wani harin bam na kunar bakin wake da aka kai jiya a birnin ya halaka akalla mutane 14 sannan sama da 70 sun samu raunuka. Galibi wadanda harin ya rutsa da su ´yan sanda ne. Bam din ya fashe ne a gaban wani otel dake kusa da masallacin nan da ake yiwa lakabi da Jan masallaci ko Red Mosque, bayan da ´yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa wasu dalibai na addini da suka mamaye masallaci ku ma suna bukatar a sako wani babban malami dake goyon bayan Taliban. A jiya juma´a dai gwamnatin Pakistan ta sake bude masallacin ga jama´a, makonni biyu bayan murkushe masu kishin Islama a cikin masallacin. Bayan rikicin na jiya gwamnati ta rufe wannan masallaci har sai abin da hali ya yi.