1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan na cikin wani hali na tsaka mai wuya

Ibrahim SaniNovember 22, 2007
https://p.dw.com/p/CQTb

Sabbin Alƙalan da aka naɗa a kotun ƙolin Pakistan, sun yi watsi da ƙarar dake ƙalubalantar takarar shugaba Musharraf. Ƙarar a cewar rahotanni na a matsayin ta ƙarshe, a jerin ƙararrakin da ´Yan adawa su ka shigar ne, don ƙalubalantar takarar ta Mr Musharraf. Hukuncin na baya-bayan nan a yanzu haka, zai bawa Mr Musharraf dama na yin ta zarce a karo na biyu a jere na tsawon shekaru biyar. Mr Musharraf a baya ya ce da zarar kotun ƙolin ta yarje yin tazarcen to zai ajiye kakinsa, tare da zamowa cikakken shugaban ƙasa na farar hula. Jam´iyyun adawa na ƙasar na ci gaba da adawa da hukuncin kotun ƙolin tare da kiran da a ƙauracewa zaɓen na gama gari. An shirya gudanar da zaɓen ne, a ranar 7 ga watan Janairun sabuwar shekara ta 2008.