1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan-Musharraf

November 27, 2007
https://p.dw.com/p/CTsS

Shugaban sojin Pakistan Pervez Musharraf, ya yi bankwana da abonkan aikinsa sojoji, kwana ɗaya kafin ya sauka daga mukaminsa na shugaban rundunar sojin kasar. Musharraf ya ziyarci shelkwatar rundunar tsaro dake birnin Rawalpindi, inda aka yi masa paredin bankwana.

Musharraf ya dauki wannan mataki na tube rigar soji, kamar yadda kasashen ketare da abokan adawa suka bukata.

Wannan matakin ya zo kwana daya kafin gobe alhamis, ranar da ake shirin rantsar da shi a matsayin zabebben shugaba, bayan alkalin kasar, ya ratabba hannu kann wani kwaskwarima da ‚yan majalisa suka yiwa kundin tsarin mulkin kasar, da ya bashi nasara kann zaben shugaban kasa da aka gudanar cikin watan oktoban da ya gabata. Za’a gudanar da zeben gama-gari ranar 8 ga watan jinairu maizuwa, amma sai dai kuma shugabannin adadawa, Benezir Bhuto da Nawaz Sherif, sun yi barazanar kauracewa zaben.