P/M Thailand Thaksin ya baiyana aniyar Murabus domin dorewar zaman lafiya a kasar | Labarai | DW | 05.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

P/M Thailand Thaksin ya baiyana aniyar Murabus domin dorewar zaman lafiya a kasar

P/M Thailand Thaksin Shinawatra ya baiyana aniyar sauka daga mukamin sa domin samun zaman lafiya a kasar, bayan matsin lamba da zanga zanga daga yan adawa dake buƙatar sai ya sauka daga mukamin sa . Shugaban gwamnatin na Thailand ya ce zai sauka daga mukamin sa bayan majalisar dokoki ta yi zaman muhawara ta kuma zaɓi sabon P/M da zai gaje shi. Shinawatra wanda ya baiyana aniyar yin murabus din a wani jawabi da ya yiwa alúmar ƙasar ta gidan talabijin, yace zai ja baya domin ya huta daga harkokin siyasa. Thaksin wanda ya hau karagar mulki a shekarar 2001 bayan samun nasarar lashe zaɓe, yace zai cigaba da zama shugaban rikon ƙwarya ya zuwa lokacin da majalisar za ta naɗa sabon P/M. A waje guda kuma yan adawa sun ce ba za su tabbatar ba tukunna har sai P/M ya yi murabus.