1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ostiriya: Za a sake gudanar da sabon zabe

Mohammad Nasiru AwalJuly 1, 2016

A wani abin da ke zama sabon kalubale ga kungiyar Tarayyar Turai EU, babbar kotun kasar Ostiriya ta bada umarni a sake gudanar da zaben shugaban kasa na watan Mayu.

https://p.dw.com/p/1JHkW
Österreich Verfassungsrichter erklären die Bundespräsidentenwahl für ungültig Verfassungsgericht
Hoto: picture alliance/dpa/L. Niesner

[No title]

Hukuncin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar ta Ostiriya na zama irinsa na farko da aka taba soke sakamakon zaben shugaban kasa kuma aka kira da sake gudanar da sabo a wata kasa ta kungiyar tarayyar Turai.

Hukuncin wanda shugaban alkalan kotun kundin tsarin mulkin kasar Ostiriya, Gerhart Holzinger ya sanar na zama wata nasara ga jam'iyar Freedom Party wato FPÖ wadda ta kalubalanci sakamakon zagaye na biyu na zaben ranar 22 ga watan Mayu bisa zargin tabka kura-kurai masu yawan gaske.

Tuni da shugaban jam'iyyar ta FPÖ Heinz-Christian Strache ya kira hukuncin da kotun tsarin mulkin Austriya ta yanke da babbar nasara ga tsarin demokradiyya.

Österreich Verfassungsrichter erklären die Bundespräsidentenwahl für ungültig Norbert Hofer
Norbert Hofer na jam'iyyar da ke kyamar baki na tsammanin wa rabbukaHoto: picture alliance/dpa/L. Niesner

Ya ce: "Demokradiyya da mulki da doka su ne suka yi nasara a yau. Al'ummar kasa ma sun yi nasara, domin suna tabbacin cewa bayan kura-kurai masu yyawa da aka tabka, kotun tsarin mulki ta ba za ta kyale ba dole a dauki mataki. Saboda haka muna maraba da hukuncin."

Gani cewa yanzu ana jiran ranar da kasar Birtaniya za ta fice daga kungiyar EU biyo bayan kuri'ar amincewa da ficewar kasar da al'ummarta suka kada a makon daya gabata, duk wata nasara da dan takarar jam'iyyar FPÖ a Ostiriya Nobert Hofer zai samu, za ta karfafa guiwar jam'iyyarsa da ma sauran irin masu ra'ayyinta a kasashen Faransa da Netherlands da ma a wasu wuraren da ke neman a rage wa kungiyar EU karfin iko ko ma a fice daga kungiyar gaba daya.

A kasar Ostiriya dai majalisar dokoki ce ke ke yanke hukunci game da kuri'ar raba gardama amma ba shugaban kasa ba, sai dai duk wata nasara da dan takarar jam'iyyar FPÖ Norbert Hofer zai samu za ta kara matsa kaimi a kasar na gudanar da zaben raba gardama kan ko kasar ta cigaba da zama cikin Tarayyar Turai. Bayan kuri'ar raba gardama a Birtaniya Hofer ya hango bukatar gudanar da kuri'ar raba gardama a cikin shekara guda idan ba bu wani sauyi na hakika a cikin kungiyar ta EU.

Banbanci ra'ayi kan soke sakamakon zaben Ostiriya

Sai dai a lokacin da yake mayar da martani bayan hukuncin kotun, shugaban gwamnatin Ostiriya Christian Kern ya ce bai ga wani abin ta da hankali ba.

Ya ce: "Ina tabbatar da cewa wannan hukuncin bai zai zama wani abin sosa rai ba ko wani abin ta da jijiyar wuya, ya nuna karara cewa tsarin demokradiyyarmu na da karfi kuma yana tafiya kan kyakkyawar turba. Ina son a yi gajeren yakin neman zabe ba tare da neman wasum kalamai masu sosa rai ba."

Österreich Verfassungsrichter erklären die Bundespräsidentenwahl für ungültig Alexander Van der Bellen
Ta leka ta koma wa Van der Bellen da ya lashe zaben OstiriyaHoto: picture alliance/dpa/L. Niesner

An dai samu mabambamtan ra'ayoyin 'yan kasar ta Ostiriya game da hukuncin. "Idan babbar kotu ta yanke wannan hukunci dole mu amince da shi. Ba zan iya cewa ko hukunci ya yi daidai ko bai yi ba."

Wannan kuwa cewa ta yi: "Na yi mamaki matuka da jin wannan duk da kura-kuran da aka samu, an kidayar kuri'u daidai , ko da yake an yi kidayar da wuri."

Hukundcin ya zo ne mako guda gabanin a yi biki rantsar da mutumin da ya lashe zaben wato Van der Bellen. ba a dai sanar da arnar da za a sake gudanar da zaben ba, kuma kafin lokacin shugabanni uku na majalisar dokoki za su tafi da ragamar shugabanci cikinsu kuwa har da Norbert Hofer, bayan shugaba mai ci Heinz Fischer ya sauka a mako mai zuwa.