1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ostiriya ta nemi a kai dakaru iyakokin Afirka

Yusuf Bala Nayaya MNA
May 28, 2018

Shugaban gwamnatin Ostiriya Sebastian Kurz ya bukaci ganin dakarun da ke kula da iyakar kasashen Turai sun fadada aikinsu a kasashen da ke arewacin Afirka saboda 'yan hijira da ke tsallako Bahar Rum don zuwa Turai.

https://p.dw.com/p/2yQpS
München MSC 2018 | österreichischer Kanzler Sebastian Kurz
Sebastian Kurz shugaban gwamnati a OstiriyaHoto: Reuters/M. Rehle

Shugaban mai ra'ayin mazan jiya ya bayyana haka ne a ranar Lahadi a tattaunawar da ya yi da jaridar Die Welt ta Jamus, ya ce dakarun da ke kula da iyakar ta Turai ya kamata su nemi dama ta yadda za su jagoranci aikin kula da iyakokin a kasashe kamar Tunisiya da Libiya don taka birki ga bakin hauren da ke biyo wadannan kasashe don shiga Turai.

Ya ce hakan ne zai sanya a kawar da aikin miyagun mutane da ke fasakaurin al'umma. Fiye da bakin haure 1500 ne dai tsakanin ranar Alhamis zuwa Juma'a da suka gabata wasu kungiyoyin sakai suka kubutar da su a teku.

A watan Yuli mai zuwa ne kasar ta Ostiriya za ta karbi jagoranci na majalisar Tarayyar Turai.