1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Olmert ya Umurci kai hare hare a Gaza

Prime ministan Izraela Ehud Olmert ya umurci sojojin kasarsa dasu fara kai hare hare akan sojojin sakai na yankin palasdinawa dake Gaza,a matsayin martani kann hare haren rokoki da palasdinawan suka harba ,wanda ya raunana wasu matasa yahudawa guda biyu,duk da yarjejeniyar tsagaita wuta dake cikin watansa na farko.Bayan ganawarsa da manyan jamian tsaro na izraelan,Mr Olmert ya bawa rundunar tsaron yankin izinin cigaba da kai hare hare zuwa zirin na gaza,ba tare da laakari da yarjejeniyar data fara aiki ranar 26 ga watan nuwamba ba.Sai dai jim kadan da zartar da wannan mataki a bangaren izraela ,mayakan sakai na palasdinun suka harba wasu rokoki zuwa yankin kudancin iazraelan.