1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obasanjo ya gana da iyalan marigayi shugaban Boko Haram

September 16, 2011

A wani mataki na kawo ƙarshen hare haren ƙungiyar Boko Haram a Najeriya, tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo ya ziyarci dangin marigayi tsohon shugaban ƙungiyar Mohammed Yusuf a Maiduguri .

https://p.dw.com/p/12an0
Tsohon shugaban Najeriya Olusegun ObasanjoHoto: dpa

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obansanjo ya buƙaci dangin marigayi shugaban ƙungiyar Boko Haram Mohammed Yusuf da magoya bayansa su dakatar da munanan hare haren ƙin jinin gwamnati da suke kaiwa wanda ke janyo hasarar rayuka da kuma zubar da jini. A ranar juma'ar nan ce tsohon shugaban Najeriyar Obasanjo ya gana da iyalan marigayin Mohammed Yusuf a birnin Maidguri. Ziyarar ta ba zata ta zo ne 'yan makonni bayan da ƙungiyar ta Boko Haram ta ayyna ɗaukar alhakin kai hari a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya dake Abuja wanda ya hallaka mutane 23 da kuma jikata wasu mutanen fiye da ɗari ɗaya. Wani jami'in kare haƙƙin bil Adama Malam Shehu Sani dake cikin tawagar da ta gana da iyalan na Mohammed Yusuf yace Obasanjo ya tattauna ta tsawon sao'i biyu da iyalan marigayin. Ganawar dai ita ce ta farko da wani shugaba ya yi da 'ya'yan ƙungiyar ta Boko Haram tun bayan kashe Mohammed Yusuf a shekarar 2009. Surikin Mohammed Yusuf, Babakura Fugu yace ganawar da suka yi da Obasanjo ta ƙara musu ƙwarin gwiwa cewa gwamnati za ta yi adalci. Yace Obasanjo ya yi alƙawarin sanar da shugaba mai ci Goodluck Jonathan dukkan abubuwan da suka tattauna wanda ya hada da buƙatar biyan diyya ga iyalan 'ya'yan kungiyar da aka kashe a farmakin jami'an tsaro a shekarar 2009.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Muhammad Nasir Awal