Obasanjo ya amince ya miƙa Charles taylor ga hukumomin Liberia | Labarai | DW | 25.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obasanjo ya amince ya miƙa Charles taylor ga hukumomin Liberia

Shugaba Olesegun Obasanjo na tarraya Nigeria ya amince ya tassa ƙeyar tsofan shugaban ƙasar Liberia, Charles Taylor, ga hukumomin Liberia, domin gurfanar da shi gaban ƙulliya.

A yau ne Obasanjo , a hukunce, ya ba sabuwar shugabar Liberia, Ellen Sierleaf Johson, damar karbar Charles Taylor, da ke gudun hijira, a Nigeria tun shekara ta 2003.

Kotun Majalisar Ɗinkin Dunia,mai shari ´ar manyan leffikan yaƙi ,da ke ƙasar Sieraleone , na zargin sa, da aikata kissan kiyasu, a lokacin yaƙin bassasar da ya ɓarke a Liberia da Saleo, wanda kuma, yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu 200.

Sanarwar da fadar gwamnatin Nigeria ta bayyana , ta ƙara da cewa, Shugaba Obasanjo, ya ɗauki wannan mataki, bayan ya tuntuɓi takwarorin sa na Afrika, mussaman shugaban ƙungiyar taraya Afrika Denis Sassun Nguesso, da kuma shugaban ƙungiyar ƙasashen CEDEAO Tanja Mamadu.

Saidai sanarwar ba ta bayyana ranar miƙa Charles Taylor ɗin ba, ga hukumomin Liberia.