1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama zai gana da Shugaban Kanfanin BP

June 15, 2010

Majalisar dokokin Amurka zata saurari bahasi daga shugabanin kanfanonin haƙan manfetur daban-daban

https://p.dw.com/p/Nqv5
Shugaba Obama yana magana ta Tarho da Firaministan Birtaniya Cameron akan matsalar BPHoto: AP

A yau ne Majalisar Dokokin Amurka zata saurari bahasi daga shugabanin kanfanin haƙan manfetur na BP da yanzu haka ɗan yen man dake ɓulɓulowa daga wani rijiyan kanfanin a tekun Mexico na Amurkan keci gaba da haifar da gurɓata yankin ruwan ƙasar.

Sauran kanfanonin da suma suka amsa sanmacin majalisar sun haɗa da kanfanonin Exxon Mobil da Shell da Kuma Chevron. Ko'a jiya sai da shugaban Amirka Barack Obama ya sake kai ziyara yankin a karo na huɗu domin ganin ƙoƙarin da akeyi na daƙile kwararan da ɗanyen a Tekun Mexico. Obama wanda ake sa ran zai yiwa Amirkawa jawabi ta kafofin yaɗa labarai game da wannan bala'i daya afkawa ƙasar, yace an cimma yarjejeniya da kanafnin na BP na biyan diyyar Biliyoyin daloli ga al'umma da kuma gwamnati na hasarar da aka tafka.

A gobe ne kuma Obaman zai gana da shugaban kanfanin na BP Carl-Henric Svanberg. Yanzu haka dai hannayen jarin kanfanin na BP naci gaba da karyewa a manyan kasuwannin hannun jari na duniya dake New York da kuma da London.

Yanzu haka kuma wani labari na cewar an samu rahoton girgizan ƙasa mai ƙarfin Maki 5.7 na ma'aunin girgizan ƙasa a wani yankin na dake kan iyakan Californiya da Mexico a ƙasar ta Amurka.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Umaru Aliyu