Obama zai fara ziyara a wasu kasashen Turai
November 13, 2016Masu aiko da rahotanni suka ce ana ganin Obaman zai yi wannan ziyara ce da zummar kwantar da hankalin kasashen bayan yakin neman zabe mai zafi da kuma zaben Donald Trump a matsayin sabon shugabann a Amirka. A lokacin yakin neman zabe da ya yi dai, sabon shugaban na Amirka Trump ya yi ta sukan tsarin tafiyar da kungiyar tsaro ta NATO da yarjejeniyar da aka cimma kan dumamar yanayi a birnin Paris da ma yarjejeniya kan nukiliyar kasar Iran.
Wani abu kuma da ke kara razana sauran kasashen musamman ma na Tarayyar Turai shi ne na matsayin da Donald Trump ya dauka dangane da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin wanda ya ce za su iya aiki tare. Yayin wannan ziyara, Shugaba Obama zai gana da shugabanin kasashen Faransa da Britaniya da Italiya kafin daga bisani ya kammala rangadin nasa daga kasar Peru inda zai halarci babban zaman taro kan tattalin arziki na kungiyar APEC na Asiya da Pacific.