Obama ya umarci kanfanin BP na Birtaniya ya biya diyya | Labarai | DW | 05.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Obama ya umarci kanfanin BP na Birtaniya ya biya diyya

Wannan ziyara da shugaba Obama yakai yankin itace ta uku tun aukuwan hatsarin a watan Afirilun bana

default

Shugaba Barack Obama na Amirka

Shugaban Amirka Barack Obama ya isa gaɓar yankin ruwan Louissiana domin jajantawa al'umomin yankin game da malalan ɗanyen manfetur da kanfanin BP ya haddasa a tekun Mexico.

Wannan ziyara da shugaba Obama yakai yankin itace ta uku tun aukuwan hatsarin a watan Afirilun bana.Obama wanda yanzu haka gwamnatin sa ke shan suka game da lamarin, shima ya soki kanfanin BP ta Birtaniya.

Obama yace mun umarci shugabannin kanfanin BP daya hanzarta biyan diyya don gane da wannan  bala'i da kanfanin su ya haddasa, kuma zamu tabbatar da cewar sun bi wannan umarni da muka bayar na tallafawa ɗokacin al'umman da wannan bala'i ya shafa ta fuskar tattalin arziki cikin gaggawa.

Yanzu haka dai kanfanin na BP ya fara anfani da wata sabuwar dabara wajen zuƙe ɗanyen man fetur dake cigaba da kwarara a yankin tekun na Amirka. yanzu haka dai kanfanin na BP ya bada sanarwar rage man dake kwararan ta anfani da wasu sabbin dabaru.

Mawallafi: Babangida Jibril, Edita: Abdullahi Tanko Bala