Obama ya samu karɓuwa a Jamus | Siyasa | DW | 20.01.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Obama ya samu karɓuwa a Jamus

Ra'ayoyi a nan Jamus dangane da Barack Obama

default

Barack Obama da Michelle Obama

Tun bayan zamanin shugaban Amurka John F. Kenedy , ba a sake samun wani shugaban daya samu karɓuwa da farin jini ciki da wajen ƙasa ba, kamar Barack Obama. Ko anan Tarayyar Jamus ma mafi yawa daga cikin 'yan siyasa sun bayyana farin cikinsu da wannan gwamnati, sai dai manazarta sun yi gargaɗin cewar ayi taka tsantsan.

Irin tarya da akayi wa sabon shugaban Amurka kenan Barack Obama, lokacin daya ziyarci birnin Berlin a karshen watan Yulin shekarata 2008. Sama da mutane dubu 200 suka yi dafifi domin marabtan Ɗan takarar kujerar shugabancin Amurkan a dandalin Siegessaäule.

Kazalika Miliyoyin Jamusawa ne suka haɗe dashi a bukin taya shi murnar nasarar zaɓen sa na 4 ga watan November. Wannan nasara da Obama ya samu ya haifar fata da zato daga ɓangarori daban-daban....

"Idan har ya cimma aiwatar da rabin abubuwan daya alkawarta, to babu shakka ana iya cewa wannan wani gagarumin matakin cigaba ne wa duniya baki ɗaya,kuma hakan abin farin ciki ne ".

Kazalika irin wannan fatan ne shugaban Jamus Horst Köhler yayi akan sabon shugaban na Amurka.

Nahostreise Außenminister Frank-Walter Steinmeier in Ägypten

Frank-Walter Steinmeier

"Wannan babbar dama ce, da za a dada samun ingantuwar dangantaka tsakanin Jamus da Amurka, saboda yana da kyawawan manufofi , domin haka wannan wata dama ce wa dukkan Jihohin dake Amurka,da tarayyar jamus dama duniya baki daya"

Abun takaici inji kwararre ta fannin kimiyyar siyasa dake nan birnin Bonn Professa Christian Hacke shine, akwai babban aiki a gabansa, musamman dangane da halin da kasarsa take ciki....

"Ya kasance mutum ne wanda ya samu karɓuwa a tsakanin jama'a, harda turawa. Kwarjininsa da irin kyawawan manufofi da yake dasu wa Amurkawa, waɗanda ana iya cewa baiwa ace a gare shi"

Shi kuwa ministan harkokin wajen tarayyar Jamus Frank Walter Steinmeier cewa yayi.

Horst Köhler hält dritte Berliner Rede ARCHIVBILD von 2007 QUER

Shugaban Jamus Horst Köhler

"Dukkannnen kudurorinsa , da suka haɗar da kalubalantar sauyin yanayi, tabbatar da kariya wa makamashi, tsarin kwance damarar yaki, kulla sabbin dangantakar aiki da kungiyoyin ƙasa da ƙasa, batutuwa ne da muke bashi goyon baya, don haka ina matukar farin cikin ganin cewar zamu samu ingantuwan aiki tare da sabuwar gwamnatin Amurka"

Waɗannan dai sun kasance kyawawan manufofi, wadanda kuma gwamnatin Bush data gabata da Jamus basu samu haɗin kan aiki tare akansu ba.A yayin ziyararsa a nan tarayyar Jamus dai, Barack Obama yayi kira dangane da kara fadada ayyukan sojojin Turai da na Jamus a kasar Afganistan. Batu da ministan tsaron jamus Franz Joseph Jung yace ba abun tsoro bane

Franz Josef Jung auf der Handelsblatt Konferenz

Dr. Franz Josef Jung,

"A ganina wannan ba wata matsala bace, abunda keda muhimmanci anan shine muna da kyakkyawar dangantakar aiki da Amurka, kuma muna fatan hakan ma zai ɗore nan gaba".