Obama ya gana da Buhari a Washington
July 20, 2015Shugaban kasar Amirka Barack Obama ya yaba da matakkan da shugaban kasar Najeriya Muhamadu Buhari yake dauka wajen yakar kungiyar Boko Haram mai yaki da makammai a kasar tun a shekara ta 2009. Obama ya yi wannan yabo ne ga shugaba Buhari lokacin ganawar da suka yi a fadar White House a mataki na farko na wata ziyarar aiki ta kwanaki da ya soma a kasar ta Amirka.
Shugaba Obama ya kuma ce a bayyane take cewar da gaske shugaba Buhari yake a shirinsa na yakar kungiyar ta Boko Haram dama duk wasu ayyukan ta'addanci da na cin hanci da karbar rashawa a Najeriya dama Afrika baki daya.Ya kuma kara da cewa za su tattauna da shugaba Buhari a kan yanda kasashen biyu za su yi aiki kafada da kafada wajen yakin da ayyukan ta'addanci dama cin hanci da rashawa a kasar ta Najeriya.