1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya ce tarihi ba zai manta da Merkel ba

Usman Shehu UsmanApril 24, 2016

Shugaban kasar Amirka ya yaba wa shugabar gwamnatin Jamus bisa kokarin da ta yi na karbar 'yan gudun hijira duk kuwa da adawar da ta fuskanta daga wasu kasashen Turai da dama.

https://p.dw.com/p/1Ibrb
Angela Merkel Barack Obama Hannover Deutschland PK
Hoto: Reuters/K.Lamarque

Barack Obama ya ce sanin kowa ne daukar irin wannan matakin ba karamin cece-kucen siyasa yake ciki ba, amma duk da haka Angela Merkel ta dage don cimma burin karbar 'yan gudun hijiran, inda shugaban kasar ta Amirka ya kara da cewa

"Angla Merkel ta fahimci bukatar mutanen da aka hana musu 'yancinsu, wadanda kuma ke neman rayuwa mai inganci. Na san cewa siyasar da ke tattare da irin wannan mai wuya ce a dukkan kasashenmu."

A cewar Obama shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, na kan hanyar kafa tarihi bisa irin jajircewar da ta yi, na bai wa 'yan gudun hijira mafaka. Domin a cewar Obama, Merkel ta yi tsayin daka na kawo abinda zai hada kan mutane komi wahalar da ke tattare da shi.

A na ta bangaren lokacin da take mayar da martani shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tabo rikicin kasar Ukraine, inda ta bayyana cewa tsagaita wuta a gabashin kasar ta Ukraine, bisa ga dukkan alamu ba ya aikin yadda aka tsara. Merkel ta ci gaba da bayani tana mai cewa:

"Muna kan bakararmu na yin aiki da yarjejeniyar Minsk, za mu kara azama don tabbatar da aiki da ka'idojin da aka cimma. Kawo yanzu ba mu da tsagaita wuta da ta dore, don haka ya zama wajibi, mu matsa lamba bisa matakan siyasa. Domin duba mataki na gaba da ake bukata don samar da zaman lafiya mai dorewa."

Angela Merkel ta bayyana cewa, a rikicin da ya mamaye gabashin Ukraine, ba wai ga kasar kadai za su dogara ba, suna shirin yin zama musamman da kasar Rasha, mai fada a ji a bangaren 'yan tawaye, kamar yadda kasashen yamma ke fada wa gwamnatin Ukraine ta ji.