1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama da Netanyahu na taro a Washington

July 6, 2010

Ana fatan zasu tattauna matsalar yankin gabas ta tsakiya

https://p.dw.com/p/OBpb
Firaministan Isra'ila Benjamin NetanyahuHoto: AP

A yaune shugaban ƙasar Amirka Barack Obama da Firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zasu gana a Washington.

Wannan ziyarar dai za ta buɗe wani sabon babi, saɓanin abin da ya faru a ziyarar farko da Netanyahu ya kai washington a watan Maris na bana, inda Washington ta nuna ɓacin ran ta da ci gaba da gine gine a yankunan matsugunana Yahudawa a yankin Palasɗinawa.

Babu dai fatan samun wani ci gaba mai yawa a ganawar tasu to amma ko ba komai, yanzu Isra'ila ta fara sassautowa, bayan matsi da tofin ala tsine da ta sha daga ƙasashen duniya bayan sojojinta sun hallaka wasu masu kaiwa Palasɗinawa agaji.

Ko'a yau sai da ministan harkokin wajen Turkiya ya nana ta kira ga Isra'ila da ta nemi gafarar kisan da Sojojin ta sukayi akan wasu Turkawa tara.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Umaru Aliyu