Obama a birnin Berlin | Siyasa | DW | 24.07.2008
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Obama a birnin Berlin

Ɗan takarar kujerar shugabancin Amurka Barack Obama ya fara ziyarar yaƙin neman zaɓe a Jamus

default

Sen. Barack Obama, da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

A yau ne Ɗan takarar kujerar shugabancin Amurka a karkashin tutar jami'iyyar Demokrat Barack Obama ya kawo ziyararsa ta farko a nan tarayyar Jamus,inda ya gana da shugabar gwamnati Angela Merkel.

Wannan ganawa ta Barack Obama wanda ke zama Ɗan majalisar Dottijan Amurkan da shugabar gwamnatin Jamus din a birnin,na zama irinsa na farko.Duk dacewar ba'a sanar da batutuwan da Tattaunawar sa'a guda ɗin ta kunsa ba,kakakin gwamnati a Berlin, Ulrich Wilhelm,sun taɓo batutuwan kasuwanci da sauyin yanayi da kuma dangantakar Amurka da kasashen turai.

Dubban mutane nedai sukayi dafifi a dandalin da Ɗan takara Barack Obama yake jawabinsa na yakin neman zaɓe.Muhimman batutuwa da yakin neman zaɓen nasa suka kunsa sun haɗar da dangantakar Amurka da ƙasashen ketare musamman turai,da manufofinsa na ketare idan ya samu nasarar haye karagar shugabancin Amurkan.

Obama wanda daga nan Berlin zai shige zuwa kasashen Faransa da Britania a cigaba da rangadin yakin neman zabensa a nahiyar turai bayan ya gama da yankin gabas ta tsakiya,ko shakka babu ya samu goyon bayan kashi uku daga cikin huɗu na jamusawa,waɗanda suke da ra'ayin jefa masa kuri'a idan da za a basu dama.

Sai dai tsohon jakadan Amurka a nan jamus a zamanin gwamnatin Bill Clinton ,John Kornblum -yana mai ra'ayin cewar wannan rangadi da Ɗan takarar kujerar shugaban Amurka akarkashin tutar jami'iyyar Demokrat yakeyi zai taimaka masa gyara inda yake da rauni....

"Obama yana da ɗan rauni a manufofinsa na siyasar ketare,amma wannan rangadi da yakeyi yanzu ,zai taimaka masa wajen dunke wannan giɓi.Na biyu kuma shine,yanzu Amurka bata da wani daraja a ketare,da manufofinsa dangane da halin da ake ciki a Iraki da Afganistan , wadanda kuma ya ziyarta,na tabbatar da cewar za a samu sauyi a karkashinsa,idan ya samu nasara"

Kafin jawabinsa gaban sama da mutane dubu 100 da suka taru a dandalin da akayiwa suna Dandalin nasara,Barack Obama ya gana da da ministan harkokin wajen na jamus kuma ɗan jami'iyyar SPD,Frank-Walter Steinmeier.

Birnin na Berlin dai a yanzu haka yana cike da 'yan jarida na ciki da wajen Jamus,waɗanda ke yaɗa wannan jawabi na yakin neman zaben na Obama.Jürgen Trittin,shine ke sgabantar wakilan jami'iyyar The Greens dake majalisar dokoki ta Bundestag....

"Nayi farin cikin ganin cewar Ba Amurke ya zo nan domin yin jawabi wa jama'a.Hakan babu shakka zai sauya dangantakar Amurka da turai,kuma a bangaremmu wannan wata alama ce ta yiwuwar aiki tare".

 • Kwanan wata 24.07.2008
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/EjEZ
 • Kwanan wata 24.07.2008
 • Mawallafi Zainab Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/EjEZ