Nutsewan jirgin ruwa a kamaru | Labarai | DW | 23.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nutsewan jirgin ruwa a kamaru

Kamerun

Mutane kimanin 130 ake zargin cewa sun rasa rayukansu,ayayinda jirgin ruwa da suke tafiya ciki ya nutse a yankin kudu maso yammacin kamaru.Rahotannin kafofin yada labarun kasar dai na nuni dacewa an tsinci jirgin daya nutsen ne a kusa da tashar jiragen ruwa na Kribi,wanda wasu masinta suka gano,bayan cimma nasaran ceto mutane 20 da hadarin ya ritsa dasu.Jirgin ruwan dai na dauke da pasinjoji 150 ne kafin nutsewar tasa,wanda ya fito daga tashar jiragen ruwa na oron dake gabashin Nigeria zuwa tashar Gentil dake kasar Gabon.Pasinjojin dai sun hadar da yan Nigeria da Burkino faso da Janhuriyar Benin da kuma Mali.