1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Norway ce mafi farin cikin al'umma.a duniya

March 20, 2017

Ranar farin ciki ta duniya rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin waiwaye kan farin cikin al'umma da wadatar arziki da wanzuwar cigaba mai ma'ana da kuma kawar da talauci a tsakanin al'umma.

https://p.dw.com/p/2Zazf
Norwegen Famileie an der Bergspitze Lofoten
Hoto: Reuters/NTB Scanpix/Nils-Erik Bjoerholt

Majalisar Dinkin Duniya ce dai ta kebe wannan rana ta 20 ga watan Maris na kowace shekara domin waiwaye kan farin cikin al'umma da wadatar arziki da wanzuwar cigaba mai ma'ana da kuma kawar da talauci a tsakanin al'umma.

Rahoto na kasa da kasa da masana tattalin arziki suka yi nazari akai ya baiyana jadawalin kasashen da al'ummominsu suka fi farin ciki a duniya, inda kasashen Norway da Denmark da Iceland da kuma Switzerland suka kasance a sahun farko, 

Kasashen da suka kasance a baya sune Siriya da Tanzaniya da Burundi da kuma jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Rahoton ya danganta farin cikin da karfin tattalin arziki ko abin da jama'a ke samu na kudin shiga da kuma alkaluman kididdiga na tsawon rai na al'ummomin kasashen.

Bugu da kari ya duba yadda mutane suke kiyasta tallafin walwala da jin dadin rayuwa da kuma yancin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.