Noman cocoa a Afirka ta yamma | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 11.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Noman cocoa a Afirka ta yamma

Kasar Cote d'Ivoire tana son cin gajiyar tashin farashin cocoa a kasuwannin duniya.

default

Noman cocoa a Cote d'Ivoire

A wannan makon ma dai da yawa daga cikin jaridun na Jamus sun sake leƙawa yankin sahel domin duba yadda ƙungiyar Alƙa'ida ta yankin Maghreb ke daɗa yaɗa angizonta a wannan yankin. A cikin rahoton da ta gabatar jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

"Ƙasar Faransa ta lashi takobin jagorantar yaƙi akan 'yan ta'addan Alƙa'ida a yankin Sahel. Wani ɗan Aljeriya dake da cikakkiyar masaniya akan halin da ake ciki ya yi nuni da cewar yaƙin da ake gwabzawa a Afghanistan shi ne ke ba su ƙwarin guiwa akan manufa. Domin kuwa idar har wata ƙasa mai ƙaƙƙarfan matsayin na soja kamar Amirka ta kasa karya alƙadarin Taliban, ina ga sauran ƙananan ƙasashe zasu iya murƙushe Alƙa'ida a yankin Sahara. A baya ga haka akwai matsaloli na siyasa, kamar dai saɓanin da ake akan yammacin Sahara, lamarin da ya sanya ba ga maciji tsakanin aljeriya da Maroko ballanta na ma a yi batu game da tattaunawa akan maganar tsaro. Ita kuwa ƙasar Mali daman ba abin da zata iya taɓukawa game da ta'addancin."

A halin da ake ciki yanzu ƙasar Guinea-Bissau, wadda ke zaman dandalin safarar miyagun ƙwayoyi daga kudancin Amirka zuwa Turai tana cikin ƙaƙa-nika-yi saboda Ƙungiyar Tarayyar Turai ta tsayar da shawarar dakatar da taimakon da take ba ta wajen kwaskware jami'an tsaronta. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi:

"A farkon wannan makon ne Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ba da sanarwa game da cewar ba zata ƙara wa'adin taimakon da take ba wa Guinea-Bissau don yin garambawul ga jami'an tsaronta ba, idan wa'adin ya kawo ƙarshensa a ƙarshen wannan wata na agusta. Dalilin haka kuwa shi ne rashin kwanciyar hankalin siyasa da ma rashin girmama aikin doka a ƙasar ta yammacin Afirka."

Ƙasar Burkina Faso ta tashi haiƙan wajen kyautata al'amuran tsafta a ƙasar kamar yadda jaridar Neues Deutschland ta rawaito ta kuma ƙara da cewar:

"Gwamnatin Burkina Faso zata kashe abin da ya kai dalar Amirka miliyan 128 domin samar da wuraren tsafta, inda kashi 54 cikin ɗari na al'umar ƙasar zasu samu makewayi da sauran abunbuwan da suka danganci tsafta ga ɗan-Adam. Domin kuwa amfani da makewayi zai taimaka wajen ƙayyade kashi 40 cikin ɗari na cutar gudawa a ƙasar. A lokacin taron ƙolin shuagabannin ƙasashen Afirka a Kampalan Uganda ne wata ƙungiya mai zaman kanta tayi kiran mai da hankali ga matsalar tsafta a ƙasashen Afirka."

A sakamakon ƙaruwar buƙata da koma bayan ayyukan noma da kuma baranda farashin koko ke daɗa hauhawa a cewar jaridar Berliner Zeitung. Jaridar ta ci gaba da cewa:

"Manoman koko a yammacin Afirka sun dogara ne kacokam akan rancen kuɗi daga bankuna kuma koma bayan rancen kan yi mummunan tasiri akan amfanin da suke nomawa. Kuma hakan ta faru a baya-bayan nan inda ba zato ba tsammani aka samu irin wannan koma baya, musamman ma a ƙasar Cote d'Ivoire, wadda ta fi kowace noman koko a duniya. Kuma kasancewar ba a samu koma-bayan yawan mabuƙata ba sai amfanin yayi ƙaranci kuma farashinsa yayi tsada matuƙa ainun."

Mawallafi: Ahmed Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu