1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Burundi ya ce zai sauka a 2020

Ahmed Salisu
June 7, 2018

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza ya sanar da cewa ba zai sake neman wani sabon wa'adin mulki ba da zarar wanda ya ke yi ya kare nan da shekau biyun da ke tafe.

https://p.dw.com/p/2z5So
Burundi Pierre Nkurunziza
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Karaba

Shugaba Nkurunziza ya bayyana batun saukarsa daga mulki ne lokacin da ya ke jawabi ga magoya bayansa da jami'an diflomasiyya a birnin nan na Gitega da ke tsakiya kasar inda ya ce zai bankwana da mulki a shekarar 2020. A watan da ya gabata ne dai aka gudanar da wata kuri'a ta raba gardama kan gyara ga kundin tsarin mulkin kasar inda aka kara wa'adin da shugaban kasa zai yi zuwa shekaru bakwai, batun da ake ganin Shugaban ya yi ne don ya cigaba da kasancewa kan karagar mulkin kasar sai dai ya ce ba shi da wannan aniya.