Nikolas Sarkozy ya sauka Tchad a kan rikicin ″l Arche de Zoe″ | Labarai | DW | 04.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nikolas Sarkozy ya sauka Tchad a kan rikicin "l Arche de Zoe"

Kotun ƙasar Tchad, ta yi belin ´yan jarida 3 , da kuma yan mata na ƙasar Spain, da ke cikin tawagar „l´Arche de Zoe“, ƙungiyar nan da ake zargi da yunƙurin safara ƙananan yara.

A yau, shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy ya ziyarci ƙasar Tchad, a game da wannan batu.

Tun jiya Kotuna a Tchad, su ka fara sauraran 8, daga turawan 16, saidai baki ɗaya, sun mussanta zargin da ake masu.

A na kyauttata zaton, shugaba Sarkozy, zai ɗauko yan jarida 3,amma gwamnatin ƙasar Spain, ta mussanta batun cewar, shugaban, zai tafo da yan matan Spain, masu ɗawainiya a cikin jirgin, da aka tsara zai jigilar yaran.