1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nikola Sarkozy

Yahouza, SadissouMay 18, 2008

Shugaban ƙasar France Nikola Sarkozy ya cika shekara guda a gadon mulki.

https://p.dw.com/p/E285
Nikolas Sarkozy ya cika shekara guda a gadon mulkin FranceHoto: AP


A kwana a tashi, shugaban ƙasar Nikolasa Sarkozy ya cika shekara guda daidai akan karagar mulki.

Shirin na yau zai yi waiwaye adon tafiya, domin mu ga narasori da kuma koma bayan da France ta samu, a tsawan wannan lokaci.

Jim kaɗan bayan da aka bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa zagaye na biyu, da ya bashi nasara, Nikolas Sarkozy ya bayyana mahimman bururukkan da yake buƙatar cimma a zamanin mulkinsa.

Zan farfaɗo da martabar aiki, tare da mutunta sandar mulki ta hanyar biyyaya tsakanin magabata da talakawa,zan yi iya ƙoƙarina, domin bunƙasa tattalin arziki, zan yi ta yadda faransawa za su ƙara kishin zucci, da kishin ƙasarsu France.

Sannan babban burina shine in haɗa kan al´ummar France, domin ta ƙara samun fahintar juna da cuɗe ni in cuɗe ka.
A game da batun haɗin kai da fahintar juna ba tare da nuna bambacin siyasa ba, da sdama daga al´umar France na nunar da cewa Nikolas Sarkozy ya kwantata gaskiya ta la´kari da yadda ya saka ƙusoshin jam´iyar PS mai adawa a cikin gwamnati kamar alal misali, ministan harakokin wajen Bernard Kouchner sannan shine yayi ruwa yayi tsaiki domin zaɓen Dominique Strauss Khan, jigo a jam´iyar PS mai adawa a matsayin shugaban asusun bada lamani na duniya IMF.

Ta fannin tattalin arziki kuwa, jawabanin baya bayan nan na Firaministan ƙasar France, Francois Fillion ya tabbatar da cewar, France ta samu ci gaba da dugu kussan 3 cikin ɗari a shekara ta 2007 sannan a farkon watanni ukku na wannan shekara, tattalin arzikin ƙasa ya ƙara bunƙasa duk kuwa da sukar da jam´iyun adawa ke wa shugaban na France.

A lokacin yakin neman zaɓe Nikolas Sarkozy ya alƙawartawa Fransawa farfaɗo da mutunci France a Ƙungiyar Tarayya Turai, bayan da Fransawa suka yi watsi da kundin tsarin muklin EU a shekara ta 2005, sannan ya bayyana aniyarsa, ta shinfiɗa dangatar kafaɗa da kafaɗa da Amurika.

Don cimma wannan buri , shugaba Sarkozy ya gana da shugaba George Bush na Amurika, da kuma takwarorinsa, na EU, kamar shugabar gwamnatin Angela Merkel da Gordon Brown na Britaniya.

A lokacin da ya kawo ziyara farko a nan ƙasar Jamus, Angela Merkel ta yaba dangata tsakanin Paris da Berlin tare da cewa:


France da Jamus, tamkar ɗan juma ne da ɗan jummai, ta la´akari da yadda nike da kyakkyawar fahinta da shugaban ƙasar ta France, nayi imanin cewar wannan dangata za ta ƙara bunƙasa .


A watan Juli na wannan sherkara, France ke karɓar jagorancin Ƙungiyar Tarrayya Turai, hukumomin ƙasar sun ambata yinamfani da wannandama domin kara samun angizo a cikin wannan Ƙungiya, tare da ɓullo da wasu sabin shirye- shirye da zumar ƙara mata inganci.

To saidai a fagen siyasar cikin gida, shugaban Nikolas Sarkozy na fuskantar matsin lamba, hata daga wanda suka goya masa baya a lokacin zaɓen shugaban ƙasa.

Ƙiddidigar jin ra´yin jama´a da cibiyoyin ƙidaya ke bayyana lokaci zuwa lokaci, na nunar da baƙin jinni da shugaban ya samu a halin yanzu, inda kashi 32 cikin ɗari kawai na jama´a ke bayana gamsuwa da sallon mulkinsa.

Suna zarginsa da kasancewa tamkar wani cali -cali , sannan ga rashin iya bakinsa.

Kabir Sani wani ɗan Niger ne dake zaune a ƙasar France na tuntuɓe sa ta wayar talho, wanda shima ya bayyana ra ´ayin a da cewar Sarkozy yayi faɗuwar toto ruwa ga wanda suka zaɓe shi.

Nikolas Sarkozy ya alkawarata daidaita sahun danganta tsakanin Afrika da France a game da haka ya kai ´yan ziyarce ziyarce a wasu ƙasashe wanda suka haɗa da Libiya, Senegal da Gabon, to saidai a cewar Kulibali wani ƙan ƙasar Cote D´Ivoire dake zaune a ƙasar France ya bayyana mu´amila tsakanin France da Afirka a ƙarƙashin mulkin Sarkozy tamakar irin yadda aka saba baya, wato mu´mila irinta kashin dankali, inda manya ke taushe ƙanana.

A ɗaya wajen ma Sarkozy ya fi sauran shugabani muni, a dalili ofishin minista na mussamman da ya ƙirƙiro mai kula da baƙin haure.Ya ƙirƙiro opishin minista mai kulla da baƙin haure, daban komai ba, face ya taƙaita yawan Afrikawa dake buƙatar shiga France .

Burin da ministan dake kula da baƙin haure ya bayyana shine ɗaukar dukan matakan da suka dace, ta hanyar taƙaita shigar baƙin da basu da takardu a France, tare kuma da korar wanda ke zaune cikin ƙasar ba bisa ƙa´ida ba.

A cewar Ƙungiyar kare haƘƙoƙin bani adama ta ƙasa da ƙasa wato LDH hukumomin France na wuce gona da iri a game da batun baƙin haure.

Hukumar LDH ,ta bayyana rahoto albarkacin cikwan shekara ɗaya na hawan Sarkozy akan karagamar mulkin France, inda tayi bitar yanayin demokradiya da kuma ´yancin bil adama a ƙarkashin mulkinsa.

Wannan rahoto ya jera shugaban France, a sahun shugabanin da suka yi ƙaurin suna, ta fannin take haƙƙoƙin jama´a a duniya.