Nijeriya za ta daina shiga aikin zaman lafiya na duniya | Labarai | DW | 03.08.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijeriya za ta daina shiga aikin zaman lafiya na duniya

Nijeriya ta ce za ta janye sojojin ta daga ayyukan zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya idan ba'a biya mata wasu buƙata ba

default

Shugaban Nijeriya Dakta Goodluck Jonathan ya yi barazanar janye dakarun ƙasar daga ɗaukacin ayyukan wanzar da zaman lafiyar da Majalisar Ɗinkin Duniya ke yi muddin dai majalisar bata sauya irin dokokin da take bi yanzu haka ba domin taimakawa kauce kissar da ake yiwa dakaru. Shugaban, wanda ke yin jawabi ga wani babban taron ƙasa - da - ƙasa akan ayyukan wanzar da zaman lafiya wanda birnin Abuja fadar gwamnatin ƙasar ke karɓar baƙunci ya ce bai shirya yin asarar ko da sojin Nijeriya guda ɗaya ba saboda rashin ingancin dokokin da majalisar ke bi.

Jonathan dai bai fayyace irin dokokin da yake buƙatar Majalisar Ɗinkin Duniya ta canza ba amma a bara kaɗai sojojin Nijeriya 7 ne suka mutu a lokacin aikin kiyaye zaman lafiya a ƙasar Sudan, kana a yanzu kuma ƙasar na da wakilci a cikin kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya.

Hakanan shugaba Jonathan ya ɗora alhakin rigingimun da nahiyar Afirka ke fama da su akan manyan ƙasashen duniyar dake ƙera makamai.

Bayanai daga shafin yanar gizon ayyukan samar da zaman lafiyar da Majalisar Ɗinkin Duniya ke yi ya nunar da cewar Nijeriya tana da sojoji 6,000 da ke yin aikin zaman lafiya a ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya a sassa daban - daban na duniya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu