1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijeriya ta yi marhabin da allurar riga kafin Malariya

Shugaban Nijeriya ya yaba da ƙoƙarin da Bill Gates ke yi na ƙirƙiro da allurar riga kafin zazzaɓin sauro

default

Shugaban Nijeriya Dakta Goodluck Jonathan ya yaba da namijin ƙoƙarin da hamshaƙin ɗan kasuwar nan ba- Amirke wato Bill Gates da kuma Uwargidarsa ke yi wajen tallafawa harkokin kula da lafiya a Nijeriya dama wasu sassa na duniya ta hanyar gidauniyar Bill da Malinda. A cikin wata sanarwar da ofishin shugaban ƙasar ya fitar bayan wata ganawar da yayi da Bill Gates Jonathan ya kuma yi marhabin lale da jin labarin cewar, gidauniyar na ƙoƙarin ɓullo da allurar riga kafin cutar zazzaɓin sauro ko kuma Malariya nan da shekara ta 2015. Hakanan shugaban na Nijeriya ya yaba da raguwar yawan waɗanda suka harbu da cutar shan Inna ko kuma Polio daga 256 a shekara ta 2009 zuwa ukku kawai a bana ya zuwa wannan lokacin da ake magana.

Shi kuwa Bill Gates wanda ya fara da yada zango a jihar Kano dake yankin arewacin Nijeriya domin nazarin irin ta'asirin da allurar riga kafin cutar ta yi, ya nuna farin cikin sa ne da irin ci gaban da aka samu a Nijeriyar - ci gaban da kuma ya danganta da cewar, am samu ne tare da haɗin gwiwar sa'a da kuma huɓɓasa daga ɗaukacin waɗanda lamarin ya shafa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu