Nijeriya ta kulla yarjejeniyar yafe mata dinbim bashin ketare dake kan ta | Labarai | DW | 17.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijeriya ta kulla yarjejeniyar yafe mata dinbim bashin ketare dake kan ta

Tarayyar Nijeriya ta sanya hannu akan yarjeniyoyin yafe mata basussuka da wasu kasashe 8 ke bin ta a wani mataki da zai kusantar da kasar ga cimma wani shirin soke bashin dala miliyan dubu 30 na ketare da ke kanta. A cikin watan oktoba da ya gabata Nijeriya ta cimma yarjejeniya da membobi 15 na kungiyar Paris Club sake sayen bashin akan kashi 60 cikin 100 wanda yayi daidai da soke bashin dala miliyan dubu 18. Wannan dai shi ne bashi mafi yawan da aka taba yafewa wata kasa a tarihin nahiyar Afirka. Jakadun kasashen Birtaniya, Amirka, Italiya, Belgium, Switzerland, Faransa, Finland da kuma Jamus suka sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin gwamnatocinsu a wani buki da aka yi a birnin Abuja a yau asabar. Nan ba da adewa ba ake sa ran cewa sauran kasashen zasu bi sahu.