1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijeriya ta ce ita ba mabaraciya bace

June 24, 2010

Nijeriya ta ce ƙawance take buƙata ba agajin ƙasashen da suka ci gaba ba

https://p.dw.com/p/O2Iu
Hoto: AP

Gwamnatin Nijeriya ta ce tana buƙatar shiga a dama da ita da kuma ƙulla ƙawance ne a wajen taron ƙungiyar ƙasashe takwas da suka ci gaba a fannin tattalin arziƙi na G8, ba wai ta miƙa kokon barar agaji ba daga gare su. Jakadan Nijeriya a ƙasar Kanada Iyowuese Hagher ya shaidawa manema labarai - jim kaɗan gabannin isowar shugaban Nijeriya Jonathan zuwa ƙasar Kanada in anjima kaɗan cewar, halartar taron ƙungiyar G8 da shugaban zai yi, ba ta da ala'ƙa da neman taimako ta kowace fuska. Jakadan na mai ra'ayin cewar, ko da shike Nijeriya ta yi na'am da irin matsaloli da ƙalubalen da suka shafi cin hanci da kuma rashin abubuwan more rayuwa a ƙasar, amma a yanzu ba za'a ce da irin matsalolin ne kawai za'a rinƙa kallon ƙasar ba.

Bayan isar sa ƙasar Kanada, da yammacin Alhamis ɗinnan ne shugaba Jonathan zai gana da wakilan wasu kamfanonin ƙasashen da ke cikin ƙungiyar G20, daga nan kuma zai yiwa manema labarai jawabi, kana ya halarci liyafar cin abincin dare tare da takwarorin aikin sa na Angola da Afirka ta kudu. Gobe jumma'a ne kuma shugaban na Nijeriya zai halarci taron ƙungiyar ƙasashe takwas dake da ƙarfin tattalin arziƙi ta G8, gabannin ya komo gida Nijeriya.

Mwallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu