1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijeriya na cikin hali na tsaka mai wuya

March 19, 2010

Najeriya na ci gaba da fama da rigingimu na siyasa da tashe-tashen hankula a sassan ƙasar daban-daban

https://p.dw.com/p/MXZY
Siyasar Nijeriya na cikin hali na tsaka mai wuyaHoto: AP

Takun saƙar da ake ci gaba da yi tsakanin Ruwanda da Faransa a game da alhakin kisan kiyashin da ya wakana a ƙasar a shekara ta 1994 da yadda ƙasar China ke ƙalubalantar ƙasashen yammaci a fafutukar ƙarfafa hulɗar ciniki da ƙasashen Afirka na daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus akan al'amuran Afirka. Amma da farko zamu fara ne da rahoton jaridar Süddeutsche Zeitung akan halin da ake ciki a Nijeriya. Bisa ga ra'ayin jaridar dai Nijeriya na cikin wani mummunan yanayi ne a halin yanzu kuma ba wanda ya san yadda makomar ƙasar zata kasance. Jaridar ta ce:

"A yayinda marubucin adabin Nijeriya Wole Soyinka ke batu a game da cewar al'amura sun kai wa mutane iya wuya a game da manufofin Nijeriya, shi kuwa shugaban Libiya Muammar Gaddafi na tattare ne da ra'ayin cewar raba ƙasar gida biyu, shi ne kawai zai ɗinke ɓarakar da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a Nijeriyar. Gwamnati dai bata da ikon shawo kan tashe-tashen hankulan da suka zama ruwan dare walau a Nijer Delta ko a cibiyar ƙasar inda ake fama da kashe-kashe na ƙare-dangi. A baya ga haka ita kanta gwagwarmayar kama madafun iko tsakanin jami'an siyasar Nijeriya tana taimakawa wajen gurgunta manufofin ƙasar baki ɗaya."

Tun bayan da shugaba Paul Kagame ɗan ƙabilar Tutsi ya kama ragamar mulkin ƙasar Ruwanda ake fama da ƙalubalantar juna tsakanin fadar mulki a Kigali da ta Elyse a Faransa a game da mai alhakin kisan kiyashin da ya afku a ƙasar shekaru goma sha shida da suka wuce. Jaridar Der Freitag tayi bita tana mai cewar:

Dorfgericht in Ruanda Gacaca
Kotun tsage gaskiya da neman sulhu a RuwandaHoto: AP

"Babban abin da ya ƙara ruwa wutar taƙaddamar tsakanin Faransa da Ruwanda shi ne kame Rose Kabuye, kakakin gwamnatin Ruwanda da aka yi a filin jiragen saman Frankfurt aka kuma danƙa ta a hannun Faransa a shekara ta 2008. Amma fa ƙasar Faransa ta kasa ba da wata takamaimiyar shaida akan zargin da take wa Kabuye kuma a saboda haka aka sake ta. A yanzu fatan da Faransa take yi shi ne a samu kusantar juna tsakanin ƙasashen biyu ta yadda zata ci gajiyar wani shirin gina madatsan ruwa tsakanin Ruwanda da Burundi da kuma Kongo."

Afirka ta samu kyakkyawan ci gaba a ƙoƙarin da nahiyar ta daƙile matsalar talauci kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito ta kuma kara da cewar:

"Daga cikin ƙasashen da suka samu wannan ci gaba har da Habasha, wadda ta samu raguwar yawan masu fama da matsanancin talauci daga kashi 80 zuwa kashi 30 cikin ɗari. To sai dai kuma a sakamakon tashe-tashen hankula a wasu sassa na nahiyar matsalar talaucin ta ƙara yin tsamari ta yadda da wuya a cimma burin Majalisar Ɗinkin Duniya dangane da shekara ta 2015."

China na ci gaba da ƙalubalantar ƙasashen yammaci wajen zuba jari a ƙasashen Afirka. Jaridar Kölner Stadtanzeiger tayi bitar dalilin haka tana mai cewar:

Kamerun China Hu Jintao in Afrika
China na ƙarfafa dangantakarta da AfirkaHoto: AP

"Ƙasar China na buƙatar ɗanyyun kayayyki sakamakon bunƙasar al'uma da take samu ba ƙaƙƙautawa. Kuma ƙasar ba ta dogara kacokam akan kasuwannin duniya ba tana zuba maƙudan kuɗi wajen hakar ma'adinai a Afirka, nahiyar da ƙasashen yammaci suka daɗe suna sako-sako da al'amuranta. Chinar ba ta gindaya wani sharaɗi muddin zata cimma biyan buƙatunta a ƙasashen na Afirka."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita:Abdullahi Tanko Bala