1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijeriya: Ganawa da manyan alkalai a fadar Aso Rock

October 6, 2017

A kokarin bude sabon babi a dangantaka da ke tsakanin bangaren zartarwa da na shari’a, manyan alkalan kotunan Najeriya sun yi wata ganawa da shugaban kasar a fadar gwamnati lamarin da ya kasance irinsa na farko.

https://p.dw.com/p/2lOtD
Walter Samuel Nkanu Onnoghen Chief Justiz für Nigeria
Hoto: Ubale Musa

Kudin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi 'yancin gashin kai a tsakanin bangaren zartarwa dana shari'a, ba kasafai ake ganin alkalai a cikin fadar gwamnatin kasar ba amma sannu a hankali wani danyen ganyen da ake ta'allakawa da mayar da ido ga bangaren shari'ar, na neman mayar da alkalan wuce makadi cikin rawa a sabo na kawancen da ke tsakanin su da fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock. Ziyarar alkalan ta zamo dama ga shugaban na neman kafa kotuna na musamman a kasar da nufin gaggauta kammala shari'un cin hanci. Shugaba Buhari ya ce akwai bukatar kara kotunan yaki da hanci a matsakaicin tsarin shari'a sannan kuma da  ware rana guda a kowane mako domin sauraron shari'un hanci a kotun ta koli dama 'yar uwarta ta daukaka kara.

Nigeria Richter Korruption
A baya an sami wasu alkalai da hannu a cin hanciHoto: Abddulkareen Baba Aminu

Ana kallon ziyarar manyan alkalan da suka ce sun isa fadar gwamnatin kasar da nufin barka da zuwa ga shugaban kasar daga nema na magani a matsayin wani abu na ba sabunba, haka kalamai na babban alkalin kasar mai Shari'a Walter Ononghen, wanda da kyar da gumin goshi ya kai ga samun tabbatar da shi a mukamin, alamu na mika wuyar alkalan ne domin yakar cin hanci. Abun jira a gani dai na zaman nisa na hadin kan da kila danyen ganyen a tsakanin gwamnatin da ke kara kusantar zabe da kuma bangaren  shari'ar da ke da jan aikin adalci ga batu na zabukan a matakai daban-daban.