1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Nijeriya bayan hadarin jirgin saman fasinja da ya halaka sama da mutane 100

Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo a yau lahadi ya kira wani taron gaggawa da shugabannin kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama da jami´an sufurin jirgin sama bayan munanan hadura 3 cikin makonni 7 da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 224 a cikin kasar. An jiyo mai magana da yawon Obasanjo, Remi Oyo na cewa shugaban da kanshi ne zai jagoranci wannan taro don nuna damuwar sa ga kamfanonin bayan hadarin jirgin saman fasinja a birnin Fatakwal a jiya asabar. Misis Oyo ta ce taron wanda za´a yi cikin lokaci kankane zai samu halarcin dukkan kamfanonin jiragen sama da ke aiki a cikin kasar da jami´an kula da sufurin jirgin sama da sauran masana harkar sufurin jirgin sama na ciki da wajen Nijeriya. A jiya mutane 103 suka mutu nan take sannan biyu suka mutu daga baya yayin da 5 suka samu raunuka a wani hadarin jirgin sama samfurin DC-9 mallakin kamfanin Sosoliso a Fatakwal dake kudancin Nijeriya.